2 Corinthians 5

Wurin Zamanmu a Sama

1Yanzu mun san cewa in an hallaka tentin duniyan nan da muke ciki, muna da wani gini daga Allah, madawwamin gida a sama, wanda ba da hannuwan mutum ne suka gina shi ba. 2Kafin nan muna nishi, da marmari a yi mana sutura da gidanmu na sama, 3don saʼad da aka yi mana sutura, ba za a same mu tsirara ba. 4Saʼad da muke zaune a cikin jikin nan na duniya, nishi muke domin matsuwar da muke sha, ba domin muna so mu rabu da jikinmu na wannan duniya ba ne, sai dai don so muke yi a suturta mu da na Sama, domin mai rai ya shafe mai mutuwa. 5Allah ne ya yi mu domin wannan, ya kuma ba mu Ruhu a matsayin abin ajiya, yana kuma tabbatar da abin da zai zo nan gaba.

6Saboda haka, kullum muna da tabbaci mun kuma san cewa, muddin muna a duniya cikin jikin nan, ana raba mu da Ubangiji. 7Rayuwa bangaskiya muke, ba ta ganin ido ba. 8Ina cewa muna da tabbaci, za mu fi so mu rabu da jikin nan, mu kuma kasance a sama tare da Ubangiji. 9Saboda haka, niyyar mu ita ce, mu gamshe shi, ko muna a duniya cikin jikin nan, ko ba mu nan. 10Gama dole dukanmu mu bayyana a gaban kujerar shariʼar Kiristi, domin kowannenmu yǎ karɓi ladan aikin da ya yi a wannan jiki, ko mai kyau ne ko marar kyau.

Hidimar Sulhuntawa

11To, da yake mun san ko mene tsoron Ubangiji yake, muna ƙoƙari mu rinjaye mutane. Yadda muke kuwa, yana sane a sarari ga Allah, ina kuma fata yana nan a sarari a lamirinku. 12Ba ƙoƙari muke mu yabe kanmu a gare ku ba ne, sai dai muna ba ku damar yin taƙama da mu ne, don ku sami amsar da za ku ba wa waɗanda suke taƙama da abin da ake gani ne, a maimakon abin da yake cikin zuciya. 13In hankalinmu a taɓe yake, ai, saboda Allah ne, in kuwa cikin hankalinmu muke, ai, saboda ku ne. 14Ƙaunar Kiristi a gare mu, ita take mallakarmu, saboda haka mun tabbata, da yake wani ya mutu saboda dukan mutane, ashe kuwa, mutuwarsu ce dukansu. 15Ya kuwa mutu ne saboda dukan mutane, domin kada waɗanda suke rayuwa kada su yi zaman ganin dama a nan gaba, sai dai su yi zaman wannan da ya mutu saboda su, aka kuma tashe shi saboda su.

16Saboda haka, daga yanzu zuwa nan gaba, ba mu ƙara ɗaukan wani mutum bisa ga ganin duniya ba. Ko da yake a dā, mun ɗauki Kiristi haka, amma yanzu mun daina yin haka. 17Saboda haka, duk wanda yake cikin Kiristi, sabuwar halitta ce, tsohon alʼamari ya shuɗe, sabon ya zo! 18Duk wannan kuwa daga Allah ne, wanda ya sulhunta mu da kansa ta wurin Kiristi, ya kuma ba mu hidimar sulhu: 19wato, Allah ya sulhunta duniya zuwa kansa ta wurin Kiristi, ba ya lissafta zunuban mutane a kansu. Ya kuma danƙa mana saƙon sulhu. 20Saboda haka, mu jakadu ne na Kiristi, sai ka ce Allah kansa yake magana ta wurinmu. Muna roƙonku a madadin Kiristi: Ku sulhuntu da Allah. 21Shi da bai san zunubi ba, Allah ya mai da shi kamar hadayar zunubi saboda mu, domin mu sami adalcin Allah ta wurinsa.

Copyright information for HauSRK